Wasu da ba a san ko su waye ba, sun kashe wani jagoran fulani, Ardo Adamu Idris Gabdo mai shekara 79 a jihar Filato.
Gabdo, wanda jagora ne a yankin Panyam da ke karamar hukumar Mangu ta jihar, an kashe shi ne a hanyarsa ta dawowa daga garin Panyam bayan ya ziyarci dagacin Panyam a ranar Asabar din da ta gabata ne.
- Sabuwar Masara Ta Karya Farashin Tsohuwa A Kasuwar Filato
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 6 Tare Da Kama Wasu A Filato
Shugaban kungiyar Miyetti (MACBAN) reshen jihar, Nuru AAbdullahi ne ya tabbatar da kisan a a ranar Lahadi.
Kazalika, Nuru ya zargi Matasan Kabilar Mwaghavul da kashe Ardo, sai dai, mai magana da yawun kungiyar ci gaban Matasan kabilar, Mista Lawrence ya karyata wannan zargin.
A nasa jawabin, Shugaban kwamtin rikon kwarya na karamar hukumar Mangu, Markus Artu, ya tabbar da afkuwar lamarin wanda kuma ya yi Allah wadai da kisan.
Ya baiwa al’ummar fulanin karamar hukumar tabbacin cewa, jami’an tsaro na kan kokarin cafko wadanda suka yi kisan don su fuskanci hukunci.
Rahotanni sun bayyana cewa, sama da mutane 300 aka hallaka a kauyuka daban-daban da ke a Mangu biyo bayan rikice-rikicen da suka afku a kwanakin baya.