Shugaba Bola Tinubu ya nada Nkiruka Maduekwe a matsayin babban darakta na majalisar kula da sauyin yanayi ta kasa, har zuwa lokacin da hukumar sa ido ta NCCC ta tabbatar da hakan. Mai taimaka wa shugaban kasa Ajuri Ngelale ne ya sanar da wannan nadin, wannan nadin ya yi daidai da ra’ayin Tinubu game da makomar masana’antar makamashi da dabarun tattalin arzikin zamani a Najeriya.
Bugu da kari, an nada Ibrahim Abdullahi Shelleng a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin kudin yanayi da hada-hadar masu ruwa da tsaki. Shelleng, wanda ke da digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Ahmadu Bello da kuma kwararriyar cibiyoyin hada-hadar kudi, zai gudanar da harkokin kudaden yanayi da huldar masu ba da tallafi.
Har ila yau, zai yi aiki a matsayin Sakataren Kwamitin tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya kan shirin kunna kasuwar Carbon ta kasa, kuma zai kasance cikin kwamitin shugaban kasa kan aiyukan sauye-sauye da shawarwarin tattalin Arziki na Zamani da yanayi.
- Shekara Daya Ta Mulki: Zaki Da Dacin Gwamnatin Tinubu
- Tinubu Ya Yi Wa Kasashen Waje Tayin Zuba Jari A Nijeriya
An nada Olamide Fagbuji a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan fasahar yanayi da ayyuka. Fagbuji, manazarcin manufofi kuma masanin kimiyyar kwamfuta, zai sa ido kan yadda ake yin dijital na hanyoyin siye a Sakatariyar NCCC. Wadannan nade-naden da ke fara aiki nan take, wani bangare ne na dabarun da shugaban kasa ya yi na samar da ci gaban masana’antu koren ci gaban da kuma ci gaba mai dorewa a Najeriya.