Shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da uwargidansa Pen Liyuan, a jiya Laraba sun aike da katin taya murnar shiga sabuwar shekara su ma ga wakilan malamai da daliban sakandare a jihar Washington ta Amurka, inda suka yi musu fatan alheri a sabuwar shekarar tare da bayyana cewa, shekarar 2025 ta nuna cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka gwabza domin fatattakar zaluncin Japan da kuma nuna wariyar launin fata a duniya.
A cikin sakon, shugaban ya bayyana cewa, a yayin da ake gwabza yakin duniya na biyu dai, kasar Sin da Amurka sun yi yaki kafada-da-kafada wajen tabbatar da zaman lafiya da adalci kuma kawancen da ke tsakanin al’ummomin kasashen biyu ta dore duk da kwazazzaban da aka tsallaka kuma za ta ci gaba da dorewa har abada.
- Yadda Jawabin Shugaba Xi Ya Fayyace Manyan Nasarorin Da Sin Ta Samu A 2024
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
Haka nan, sakon ya bayyana fatan matasan kasar Sin da na Amurka za su ci gaba da shiga cikin shirin gayyato matasa 50,000 domin musayar karatu a tsakanin kasashen biyu na tsawon shekaru biyar, domin karfafa cudanya da huldodinsu na musaya a tsakanin juna, da kara fahimtar juna, da gadon kawancen al’adu da kuma ci gaba da bayar da gudunmawa ga habaka zumuncin Sin da Amurka da zaman lafiyar duniya.
Tun da farko dai, wakilan malamai da daliban sakandare na kungiyar matasan da suka shiga cikin shirin musayar karatu na matasan Sin da Amurka mutum 50,000 na tsawon shekaru biyar, sun aike da sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar 2025 ga Shugaba Xi Jinping da uwargidansa da kuma daukacin al’ummar kasar Sin. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)