A gabannin shekara ta 2025, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara, ta kafar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG da kafar sadarwar intanet, inda ya takaita wasu muhimman abubuwan da suka wakana a kasar Sin da ma duniya baki daya a shekarar dake karewa wato 2024, tare da yi wa kowa fatan cimma burinsa, da samun walwala da zaman jin dadi da kwanciyar hankali.
Xi Jinping ya siffanta shekara ta 2024 da mai cike da abubuwan burgewa, da abubuwan da ba za’a iya mantawa da su ba, da jimloli biyu, wato “mun wuce yanayin bazara, da yanayin zafi, da yanayin kaka, da kuma yanayin hunturu tare, kuma mun haye wahalhalu da cimma nasarori tare”, inda kuma ya yi amfani da wasu alkaluma guda uku don shaida nasarorin da kasarsa ta samu a wannan shekara. Na farko, bisa hasashen da aka yi, jimillar GDPn kasar zai zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 130, al’amarin da ya nuna murmurewar tattalin arzikin kasar. Na biyu shi ne, yawan hatsin da aka samu a dukkanin fadin kasar Sin ya wuce kilogiram biliyan 700, al’amarin da ya sa al’ummar kasar suka kara samun abinci. Na uku kuwa shi ne, yawan motoci dake aiki da sabbin makamashi da kasar ta kera ya zarce miliyan 10, al’amarin da ya shaida bullar wasu sabbin sana’o’i da ayyuka da salo.
- Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024
- Sin Ta Kafa Manya Da Matsakaitan Yankunan Ban Ruwa 7,300
Shugaba Xi ya kuma ayyana ziyarce-ziyarcen da ya yi a cikin kasar Sin a shekara ta 2024, inda ya nuna jin dadi sosai, ganin yadda al’ummar kasar ke morewa, gami da nuna gamsuwa ga rayuwarsu. Xi ya ce, duk yadda wani abu yake shafar wani iyali, ko wata kasa, ko kuma sassan kasa da kasa, yadda al’umma za su ji dadin zaman rayuwarsu shi ne muhimmin aiki na farko da kasar Sin take sanyawa a gaban komai.
Game da halin da ake ciki a duk duniya, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, duniya na fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice a halin yanzu, kuma a matsayinta na babbar kasa dake daukar nauyi a wuyanta, Sin na himmatuwa wajen kawo sauye-sauye ga tsarin tafiyar da harkokin duniya, da zurfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma tana kokarin zurfafawa, gami da inganta ayyukan da suka shafi shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da gudanar da taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC cikin nasara. A wasu taruka dake kunshe da bangarori biyu, ko kuma bangarori da dama, kasar Sin ta bullo da manufofinta na hakika, domin kara sanya kuzari ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.
Shugaba Xi yana cike da imani a yayin da yake hangen nesa ga shekara mai kamawa wato 2025, inda ya ce, a shekara ta 2025, kasarsa za ta kammala shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, kuma yadda ake kokarin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, tabbas zai samar da kyakkyawar makoma ga ayyukan zamanintar da kasar Sin. Kaza lika, kasar Sin za ta kara kyautata ayyukan raya zaman al’umma, da daidaita batutuwa manya da kanana na al’umma, ta yadda kowa zai kara farin ciki da walwala.
Shugaba Xi ya ce, yayin da ake gaggauta samun manyan sauye-sauyen yanayin da ake ciki a duniya, kamata ya yi sassan kasa da kasa su kai zuciya nesa, su mai da hankali a kan makomar dan Adam. Kasar Sin na son yin kokari tare da sassan kasa da kasa, wajen zama masu hadin gwiwar sada zumunta da juna, masu sa kaimin musayar wayewar kai, kuma masu gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam, don samar da kyakkyawar makomar duniya. (Murtala Zhang&Lubabatu Lei)