A jiya Laraba ne daya bayan daya ne, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS ya yi rangadi a yankunan birnin Jinhua da na Shaoxing na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin.
A lokacin da yake ziyara a birnin Jinhua a safiyar Laraba, Xi ya ziyarci wani kauye da kasuwar cinikayya ta kasa da kasa dake garin Yiwu dake karkashin birnin Jinhua, domin gane ma idanunsa ci gaban masana’antu na musamman na cikin gida, da kokarin inganta farfado da yankunan karkara, da bunkasa cinikayyar waje, da samun ci gaba mai inganci.
Sannan, da yammacin jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a yankin birnin Shaoxing na lardin Zhejiang. Yayin da ya kai ziyara dakin nuna dabarun raya tattalin arziki na gundumar Fengqiao, ya waiwayar yadda aka bullo da wannan dabara, da fahimtar yadda ake yin kirkire-kikire bisa wannan dabara.
Ban da wannan, ya kuma kai ziyara lambun shan iska na al’adar koramar Zhedong, don fahimtar tarihin koramar, da yadda ake kiyaye koramar, da ginin lambun shan iskan da sauransu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau Alhamis cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake ziyara a lardin Zhejiang, zai halarci bikin bude gasar wasannin Asiya karo na 19 da za a kaddamar da shi a birnin Hangzhou, fadar mulkin lardin Zhejiang a ranar 23 ga watan Satumba. (Masu Fassara: Mohammed Yahaya, Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp