A yau Laraba ne shugaban kasar Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude dandalin sada zumunta tsakanin al’ummun Sin da na Amurka da ke da taken “Alaka da Kuliang”, inda a cikin sakon na sa ya jaddada cewa, tushen ci gaban alakar sassan biyu ya ta’allaka ne kan hadin kan al’ummunsu.
Kaza lika shugaba Xi ya yi fatan cewa, dukkanin al’ummun sassan biyu za su yayata labarin “Kuliang”, tare da ingiza ma’anar sa, ta yadda zumuntar dake tsakanin Sin da Amurka zai ci gaba da wanzuwa yadda ya kamata.
A shekarar 1901, iyayen wani jariri Ba’Amurke mai suna Milton Gardner, sun zo da shi birnin Fuzhou na kasar Sin. Kuma a shekarar 1911, shi da iyalansa suka koma Amurka. To sai dai bayan hakan mista Gardner ya ci gaba da kaunar sake komawa garin sa dake kasar Sin, amma bai samu zarafin yin hakan ba har ya rasu.
Da taimakon wasu daliban kasar Sin da ke dalibta a Amurka, uwar gidan Gardner ta gano garin da marigayi mijin ta ke fatan ziyarta a kasar Sin shi ne Kuliang dake Fuzhou.
A shekarar 1992, shugaba Xi Jinping, wanda a lokacin shi ne sakataren kwamitin JKS reshen birnin Fuzhou, ya samu wannan labari mai taba zuciya game da Kuliang, don haka ya gayyaci uwar gidan Gardner da ta ziyarci kasar Sin.
A shekarar 2012, lokacin da Xi Jinping ke matsayin mataimakin shugaban kasar Sin, ya ziyarci Amurka, inda ya ba da labarin Kuliang yayin liyafar da kawayen Sin dake Amurka suka shirya, labarin da ya yi matukar jan hankali al’ummu masu yawa daga sassan kasashen 2.
Dandalin sada zumunta tsakanin al’ummun Sin da Amurka ya gudana a birnin Fuzhou fadar mulkin lardin Fujian a yau Larabaa. (Saminu Alhassan)