A ranar Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da rubutaccen jawabi ga taron jagororin masana’antu da kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik ko APEC a takaice, a birnin San Francisco na kasar Amurka.
Shugaba Xi ya ce shekaru 30 da suka gabata, jagororin yankin Asiya da Fasifik, bisa burin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, sun gudanar da kwarya-kwaryar taro na farko na shugabannin APEC, da nufin ingiza ci gaba, da hade sassan tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik da na sauran sassan duniya, ta yadda hakan ya dora yankin kan turba ta gaggauta samun ci gaba, tare da taimakawa yankin wajen zama cibiyar bunkasar tattalin arzikin duniya.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa,duniya ta shiga wani sabon lokaci na tangal tangal da sauye sauye, kana ina za a dosa wajen aiwatar da hadin gwiwar yankin Asiya da Pasifik nan da shekaru 30 masu zuwa, ta zama sabon batu dake jan hankali a wannan lokacin da muke ciki. Dole ne mu mara baya ga ainihin burin hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik ko APEC, kana mu ingiza sabon kuzari ga hadin gwiwar kungiyar.
Ya kara da cewa, ya zama wajibi mu hada karfi da karfe wajen tabbatar da nasarar manufofi, da ka’idojin dake kunshe cikin tsarin dokokin MDD, mu nacewa turbar tattaunawa ba tare da fito na fito ba, mu wanzar da ci gaba da daidaito a yankin Asiya da Fasifik. Bai dace ba, kuma yankin Asiya da Fasifik ba zai taba zama sansanin aiwatar da siyasar shiyya ba, ballantana ya shiga wani sabon yanayi na “Cacar baka”, ko zama fagen fito na fito. Ya zama wajibi mu rungumi yanayin bude kofa na yankin mu, kuma sannu a hankali mu wanzar da tsarin ingiza matakan kafa yankin ciniki maras shinge na Asiya da Fasifik, da hade sassan tattalin arzikin yankin, kana mu samar da budadden tsarin tattalin arziki na Asiya da Fasifik ta hanyar hadin gwiwar cimma moriya tare.
Xi ya jaddada cewa, tun farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da murmurewa, kuma ana kara samar da ci gaba mai inganci, al’amarin da ya sa har yanzu Sin ta zama kasa mafi girma ga ci gaban duk duniya. Ya ce, “Bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na dogon lokaci, bai sauya ba, kana ba zai sauya ba. Muna da yakini da kwarewa sosai wajen samar da ci gaba mai dorewa, kana kuma sabon ci gaban kasar Sin zai kara samar da sabon kuzari, da sabbin damammaki ga duk duniya. Kasar Sin na kokarin raya kanta, da fadada bude kofarta ga kasashen waje, da himmatuwa wajen kirkiro wani yanayin kasuwanci na bin doka da oda, wanda ya shafi kasa da kasa, al’amarin da ba zai sauya ba, kana kuma kasar ba za ta sauya manufarta ta samar da kyawawan hidimomi ga baki masu zuba jari ba. Babban makasudin zamanantar da kasar Sin bisa salon kanta shi ne, kara samar da jin dadi ga al’ummar kasar da yawansu ya zarce biliyan 1.4, wanda zai samar da babbar kasuwa, da zarafin hadin-gwiwa ga duk duniya, da sanya babban kuzari ga zamanantar da duniya baki daya”.
Xi ya kuma yi maraba da mutane daga bangarorin masana’antu da cinikayya na duk duniya, su shiga cikin kokarin zamanantar da kasar Sin, don more damammakin ci gaban kasar mai inganci.(Saminu Alhassan, Murtala Zhang)