A ranar Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, da kuma shugaban kasar Argentina Javier Milei a gefen taron kolin kungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
Yayin ganawarsa da shugaban kasar Faransa, Xi ya ce, Sin da Faransa manyan kasashe ne dake da cikakken ‘yancin kai dake sauke nauyin dake wuyansu, huldarsu na da babbar daraja a bangaren manyan tsare-tsare da babbar ma’ana a duk fadin duniya. Ya kamata, bangarorin biyu su zurfafa cudanya ta fuskar manyan tsare-tsare da kara goyawa juna baya, ta yadda za a tabbatar da bunkasuwar huldar kasashen biyu mai dorewa da yakini, don taka rawar gani kan raya huldar Sin da Turai yadda ya kamata da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.
- Pep Guardiola Ya Tsawaita Kwantiragi A Manchester City Har Zuwa Shekarar 2027
- Sin Tana Fatan Raya Duniya Mai Adalci Dake Samun Bunkasuwa Tare Tsakanin Mabambantan Bangarori
Haka kuma, a yayin ganawarsa da shugaban gwamnatin kasar Jamus, Xi Jinping ya bayyana cewa, akwai bukatar kasashen Sin da Jamus su duba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na dogon lokaci bisa manyan tsare-tsare. Ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa ta gaskiya, mai zurfi da kyakkyawar sakamako yayin ziyarar da Scholz ya kawo kasar Sin a watan Afrilu. Yana mai cewa, a cikin watannin da suka gabata, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya samu sakamako mai ma’ana a fannonin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da sufuri mai dorewa, da hadin gwiwar raya aikin gona a Afirka, yayin da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da nuna sabon karfi da kuzari.
Bugu da kari, a yayin ganawarsa da shugaban kasar Argentina, Kasashen Sin da Argentina sun yi alkawarin ba da goyon baya wajen inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Da yake karin haske game da makomar hadin gwiwar da za a yi gaba, Xi ya ce, tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Argentina sun yi matukar dacewa da juna, yana mai bayyana fatan bangarorin biyu za su iya fadada hadin gwiwa a fannonin makamashi, da samar da ababen more rayuwa na ma’adinai, da aikin gona, da kimiyya da fasaha, da tattalin arziki na dijital. (Mai Fassara: Amina Xu, Mohammed Baba Yahaya)