Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada aniyar kasarsa na cigaba da tallafawa fannin kimiyya da fasaha bisa ikon da kasar ke da shi a kashin kanta, tare da bayyana aniyar kasar Sin na kara bunkasa ci gban kasa ta hanyar dogaro da kanta, da tsayawa da kafafunta, da kuma kiyaye tsaron ci gaban kasar.
Xi ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata a lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa Wuhan, babban birnin lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin. (Ahmad Fagam)