Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karbi takardun wakilcin kasashe da dama daga jakadun kasashe 70 da ke kasar Sin, ciki har da jakadan jamhuriyar Nijer da ke kasar Garba Seyni.
An dai gudanar da bikin mika takardun ne da yammacin jiya Litinin, a babban dakin taron jama’a da ke nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, kuma bayan bikin, Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga jakadun, inda ya jaddada cewa, yanzu haka kasar Sin na kan sabuwar hanyar zamanintar da kanta bisa tafarkin gurguzu, a wani kokari na farfado da al’ummar kasar.
Kaza lika kasar za ta nace ga bin hanyar ci gaba cikin lumana, da ma manufar bude kofarta ga ketare, don ta kara samar da damammaki ga kasashen duniya bisa bunkasuwarta.
Ya ce kasar Sin na son hada kan kasa da kasa wajen tabbatar da shawarar raya duniya, da ta kiyaye tsaron duniya, da kuma shawarar wayewar kan duniya, don inganta fahimtar juna, da kaunar juna a tsakanin al’ummar kasa da kasa, ta yadda za su fuskanci kalubalen bai daya da ke gabansu, tare da dada samun ci gaba a fannin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Lubabatu Lei)