Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasar sa a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Rasha a fannin makamashi. Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, cikin sakon da ya aike ga taron dandalin cinikayyar makamashi na Sin da Rasha karo na 4, ya ce hadin gwiwa a fannin makamashi muhimmin jigo ne na hadin gwiwar sassan 2, kuma muhimmin karfi dake iya tabbatar da isasshen makamashi a duniya.
Cikin wasikar tasa, shugaban na Sin ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar hadurra da kalubale daga sassan waje, Sin da Rasha sun karfafa tuntubar juna, tare da ingiza ayyukan hadin gwiwa, wanda hakan ke nuni ga juriyar da hadin gwiwar su ke da ita a fannin makamashi, da ma sauran manyan abubuwan da suka sanya gaba cikin hadin gwiwarsu, bisa manyan tsare-tsare a sabon karni. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp