Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya yabawa kamfanonin kasar Sin sakamakon zuba jarinsu a kasar ta kudancin Afrika.
Mnangagwa ya yi wannan yabo ne a jawabin da ya gabatar yayin rangadin duba aiki a wani kamfanin siminti na Sino-Zimbabwe dake yankin Gweru, inda ya yabawa kamfanin bisa yadda yake fadada ayyukansa a kasar Zimbabwe.
Shugaban ya ce, yana yabawa masu zuba jari daga jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda kamfanin siminti na Sino-Zimbabwe ya zuba jarinsa a kasar ta Zimbabwe.
A halin yanzu, kamfanin na Sino-Zimbabwe, yana aiki da ya kai kaso 90 bisa 100, kuma shi ne kamfani na uku mafi girma dake samar da siminiti a Zimbabwe.
Mnangagwa ya ce, tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya fara samun sauye-sauye daga tsayawar da ya yi zuwa samun bunkasuwa, kuma gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan janyo hankalin masu zuba jari don habaka ci gaban tattalin arzikin kasar. (Ahmad)