Shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, ya jinjinawa gudummawar kasar Sin, bisa yadda a shekarun baya-bayan nan ta gabatar da jerin shawarwari, ciki har da na gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama, da shawarar tabbatar da tsaron kasa da kasa, da ta bunkasa ci gaban duniya, da ta raya wayewar kan duniya.
Shugaba Tokayev, ya yi matukar yabawa wadannan shawarwari ne a wata tattaunawar sa da kafar CMG ta Sin, yana mai cewa, wadannan shawarwari sun ba da gudummawa mai armashi ga gina duniya mai daidaito da kyakkyawar makoma, kuma hakan zai haifar da ci gaban duniya mai ma’ana. Shugaban ya kara da cewa, ya zama wajibi duniya ta kubuta daga nuna wariya, da takunkumai da murgunawa. Ya kamata a zurfafa kawance, da hadin gwiwa karkashin yanayi na fatan samun alherai.
Bugu da kari, shugaba Tokayev ya bayyana kyakkyawan fatan sa ga taron dake tafe na Sin da kasashen tsakiyar Asiya, wanda zai gudana a birnin Xi’an.
Ya ce Sin na taka muhimmiyar rawar gani a yankin tsakiyar Asiya. Kuma kasashen yankin sun ci gajiya mai yawa daga alakar su da Sin, za kuma su yi duk mai yiwuwa wajen zurfafa hadin gwiwa da junan su. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp