Shugaban Kenya William Ruto, ya sanar da korar dukkanin ministocinsa sakamakon boren da gwamnatinsa ta fuskanta daga jama’a saboda tsadar rayuwa.
A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta kafar talabijin, Ruto ya ce wadanda korar ba ta shafa ba su ne mataimakin shugaban kasa Rigathi Gachagua da kuma ministan harkokin waje Musalia Mudavadi.
- Badakalar Kudade Fiye Da Miliyan 37: Kotu A Kebbi Ta Umarce CSP Rano Ya Nemo Shaidun Kare Kansa
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli Ta Ba Ƙananan Hukumomi ‘Yancin Cin Gashin Kansu
Al’ummar Kenya dai, sun kalubalanci gwamnatin kasar da rashin iya jagoranci, inda suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da kuma ta adawa da sabon harajin da gwamnati ta yi shirin dora musu, har ta kai ga rasa rayuka.
Ana ta rade-radin cewa shugaban na shirin kafa wata sabuwar karamar gwamnati ne sakamakon zanga-zangar da aka kwashe makonni ana yi.
Shi dai, Ruto ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan ya saurari jama’a, kuma nan take zai shiga tattaunawa mai zurfi a mabambantan bangarori da jam’iyyun siyasa da sauran al’ummar kasar domin kafa gwamnatin da za ta wakilci kowa da kowa.
Ya kara da cewa hakan ya zama wajibi ne domin hada karfi da karfe wajen kai wa kasar ga tudun mun tsira, sakamakon katutun matsalolin tattalin arziki da walwalar jama’a da suka dabaibaye ta.