Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, Isah Jere Idris ya sanar da karin girma ga jami’an hukumar su 4,526 da suka yi jarrabawar karin girma da wadanda suka samu horaswa daban-daban ta daga darajar mukami a shekarar 2021.
Tabbatar da karin girman na kunshe ne a cikin wasikar da ta zo daga Hukumar Gudanarwar Rundunonin da ke karkashin Ma’aikatar Cikin Gida da aka yi wa lambar CDCFIB/S.33/BOLIII/54 mai dauke da kwanan wata,18 ga Agusta, 2022.
- Malam Yaya Siffar Wankan Janaba Take?
- Jami’an Kashe Gobara Sun Ceto Mutum 91 Da Dukiyar Da Ta Kai Kusan Naira Miliyan 25 A Kano
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a yau a hedikwatarta yayin da yake yi wa wasu jami’ai masu taimaka masa da ke cikin ma’aikatan da aka yi wa karin girma ado da sabbin mukamansu.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS, wanda shi ma aka kara masa girma daga karamin Mataimakin Kwanturola (ACI) zuwa Babban Mataimakin kwanturola (DCI), Amos Okpu, ta ce jami’ai masu mukamin karamin mataimakan Kwanturola 145 sun samu karin girma zuwa Babban Mataimakin Kwanturolan Shige da Fice; sannan masu mukamin Babban Sufiritanda 99 sun samu karin girma zuwa karamin mataimakin Kwanturola.
Bugu da kari, akwai masu mukamin Sufiritanda 307 da aka mayar da su matsayin Babban Sufiritanda; kana mataimakan Sufiritanda 338 sun samu ci gaba zuwa matsayin Sufiritanda.
Sauran wadanda suka samu karin girman su ne jami’ai 589 da aka ciyar da su gaba zuwa mukamin mataimakin Sufiritanda na daya (I), sai wasu 794 da aka kara musu mukami zuwa Mataimakan Sufiritanda na biyu (II).
Har ila yau takardar ta yi bayanin cewa, jami’ai masu mukamin Sufeto 21 sun samu ci gaba zuwa mataimakin Sufiritanda na biyu (II).
Yayin da wasu jami’ai 1254 suka sami ci gaba zuwa matsayi na Mataimakin Sufeto na biyu (II), kana akwai jimillar kananan jami’ai 979 da suka samu kwarewar aiki da aka daga darajarsu zuwa matsayi na Mataimakin Sufiritanda na biyu.
Da yake jawabi a wajen bikin adonta mukarrabansa, Shugaban NIS CGI Isah Jere Idris ya yaba wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda kuma ya zama shugaban hukumar gudanarwar rundunonin da ke karkashin ma’aikatar bisa jajircewarsa wajen ciyar da ma’aikata gaba.
Ya bukaci sabbin jami’an da aka kara musu girma da su kara kwazo da saka karamcin da aka yi musu ta hanyar sadaukarwa da kuma biyayya a bakin aiki.
Ya kuma bai wa gwamnati tabbacin cewa hukumar a karkashinsa za ta ci gaba da bayar da gudunmawa mai amfani ga zaman lafiya da ci gaban kasa.
Daga cikin jami’an da aka yi wa ado da sabbin mukamansu akwai Jami’in hulda da jama’a na NIS Amos OKPU, wanda aka kara wa girma zuwa DCI; da Jami’in kula da tsare-tsare na Kwanturola Janar MY Dutse mai barin gado da magajinsa MA Ajimobi wanda a yanzu suka zama Manyan Mataimakan Kwanturola.
Sauran sun hada da Mercy Gadzama, Manajar Kula da Cibiyar Fasaha ta NIS, da a yanzu ta zama Babbar Sufiritanda, da Jami’in Tsaro na Kwanturola Janar AO Olukoya, da aka kara masa girma zuwa mukamin Babban Sufiritanda da Tanko Godiya da Nguar Loice Titus na Sashen Kai daukin Gaggawa (RRS), duka biyu da aka kara musu girma zuwa mataimakan Sufiritanda na Shige da Fice (II).