• English
  • Business News
Monday, August 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban NPA Dantsoho Ya Bayyana Aniyar Inganta Ayyukan Hukumar A Wannan Shekarar

by Sulaiman
3 months ago
in Tattalin Arziki
0
Shugaban NPA Dantsoho Ya Bayyana Aniyar Inganta Ayyukan Hukumar A Wannan Shekarar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa, Hukumar za ta cimma burinta na gudanar da ayyukanta a sa’oi 24, a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.

A cewasa, Hukumar za ta iya ciyar da ayyukan na ta gaba ne, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.

  • Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati
  • Amfani Da Karfin Gwamnati Kan ‘Yan Adawa Zai Jawo Wa Tinubu Illa A 2027 – Sule Lamido

Ya bayyana haka ne, a taro karo na biyar biyar na masana’antar JournalNG Port Industry da ya gudana a jihar Legas

Taken taron shi ne: Cike Gibi Domin A Cimma Gudanar Da Ayyuka a Sa’oi 24 A Tashar Jiragen Ruwa.

Dantsoho ya kara da cewa, hakan na daga cikin namjin kokarin da ake yi, na wanzar da tsarin PCS, a Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasar, musamman domin hakan, ya tafi kafada da kafada da na sauran kasashen duniya, ta hanyar kara habaka gasa a hada-hadar kasuwancin duniya.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta

Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island.

Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki.

Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24.

Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa, Rundunar ‘Yansanda ta kasa da kuma Hukumar Kula da Tsaro da sufurin jiragen Ruwa ta Kasa NIMASA musamman domin a kara karfafa samar da tsaro da kuma bai wa ma’aikatan Hukumar kariya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi

Next Post

Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon

Related

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji
Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

1 day ago
Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta
Tattalin Arziki

Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta

2 days ago
Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa
Tattalin Arziki

Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa

3 days ago
Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA
Tattalin Arziki

Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA

1 week ago
Dangote
Tattalin Arziki

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

2 weeks ago
Afrika Ta Zama Kasuwar Sayar Da Man Fetur Mara Inganci – Dangote
Tattalin Arziki

Afrika Ta Zama Kasuwar Sayar Da Man Fetur Mara Inganci – Dangote

3 weeks ago
Next Post
Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon

Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon

LABARAI MASU NASABA

Yadda Al’ummar Da Ke Zaune Da ‘Yan Bindiga Ke Rayuwa A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara

August 4, 2025
Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi

Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi

August 4, 2025
Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC 

Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC 

August 4, 2025
Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina

August 3, 2025
Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi

August 3, 2025
Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?

Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?

August 3, 2025
Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21

Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21

August 3, 2025
An Fara Bayar Da Hidimomin Da Suka Shafi Sauka Da Tashi Domin Gasar Wasanni Ta Duniya Ta Chengdu

An Fara Bayar Da Hidimomin Da Suka Shafi Sauka Da Tashi Domin Gasar Wasanni Ta Duniya Ta Chengdu

August 3, 2025
Rikici Ya Ɓarke A Zaɓen Ribas, Ƴan PDP Sun Fito A Matsayin Ƴan Takarar APC

Rikici Ya Ɓarke A Zaɓen Ribas, Ƴan PDP Sun Fito A Matsayin Ƴan Takarar APC

August 3, 2025
Ana Gaggauta Ayyukan Gyara Tituna Da Gadojin Da Ambaliya Ta Lalata A Arewacin Kasar Sin

Ana Gaggauta Ayyukan Gyara Tituna Da Gadojin Da Ambaliya Ta Lalata A Arewacin Kasar Sin

August 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.