Mazi Okechukwu Isiguzoro, wani shugaba a ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa mafarauta 16 daga Arewa a Uromi, Jihar Edo. A cewarsa, waɗanda suka aikata wannan mugun aikin ba ‘yan ƙabilar Igbo ba ne kuma ba su da alaƙa da al’ummar Igbo.
Isiguzoro ya bayyana juyayinsa ga gwamnonin Arewa, da mai alfarma Sarkin Musulmi, da Sarakuna, da kuma ƙungiyoyin kamar Arewa Consultative Forum da Ƙungiyar Dattawan Arewa, yana kira ga ƙwararran matakai na wayar da kan al’umma musamman matasa game da asalin mazaunan Uromi na ƙabilar Esan.
- Gwamnatin Edo Za Ta Binciki Kisan Matafiya ‘Yan Arewa A Jihar
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Kamo Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
“Al’ummar Igbo sun damu da yadda ake ƙoƙarin danganta wa Igbo laifin da suka faru a Uromi. Mun yi Allah-wadai da kisan mafarautan Arewa, amma muna ƙin danganta Igbo da wannan mugun aiki saboda yana iya haifar da rikici,” in ji Isiguzoro.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da shugabannin Arewa su hana kowane mummunan ramuwar gayya ga ‘yan Igbo da ke zaune a Arewa, yana mai nuni da buƙatar kiyaye zaman lafiya yayin bikin Sallah.
Isiguzoro ya ƙara da cewa,
“Muna goyon bayan shugabanni da sarakuna wajen rage tashin hankalin da ke faruwa a wasu garuruwan Arewa. Gudunmawarsu na da muhimmanci wajen samar da sulhu da fahimtar juna a wannan lokacin mai cike da tashin hankali.”
Ya kuma jaddada buƙatar yin watsi da duk wani nau’i na tashin hankali, ko da wane irin ƙabila ne ya aikata shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp