Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba.
Bisa ci gaban Sin cikin sauri, wasu kasashe suna daukarta a matsayin wata “barazana”. Game da hakan, Zardari ya ce, a matsayin makwabciyar kasar Sin, kasar Pakistan ta san a ko da yaushe Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, kila ne a ji tsoron sauran kasashen duniya, amma ba kasar Sin ba. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp