Shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Yamma, Hon. Soji Adagunodo, ya rasu.
Da yake sanar da rasuwar Hon. Adagunodo a wani sako da aka saki a ranar Talata da safe, dansa, Oluwatukesi Adagunodo, ya ce mahaifinsa ya rasu yana da shekaru 62.
- FAAN Ta Bai Wa Kamfanonin Jirage Umarnin Kwashe Jiragensu Daga Filin Jirgin Saman Abuja
- Wani Babban Dalilin Da Ya Haifar Da Hargitsi A Kasar Sudan
Adagunodo wanda tsohon shugaban jam’iyyar ne a Jihar Osun, ya kuma taba zama dan majalisa a majalisar dokokin jihar wanda ya wakilci mazabar jihar Obokun.
Sai dai ba a gano musabbabin mutuwarsa ba kamar yadda ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ce ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.
Majiyar iyalinsa sun tabbatar da rasuwarsa a Amurka.
A cikin sakon ta’aziyyarsa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun, ya bayyana kaduwarsa da labarin rasuwar shugaban jam’iyyar, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin “rashi mai zafi ba ga jam’iyyar kadai ba, har da Jihar Osun.”
Gwamna Adeleke ya bayyana rashin Hon. Adagunodo ya bayyana gudunmawar da ya bayar ga PDP ga ayyukan da ya yi daban-daban.
“Marigayi Hon. Adagunodo abokina ne da na goyi bayan ya zama Shugaban jam’iyyar PDP na Jiha wanda kuma shi ne ya bani goyon bayan na zama Sanatan Tarayya, babban rashi ne kuma za mu yi kewarsa matuka.
“Labarin rasuwar Honarabul Adagunodo ya yi matukar bata min rai a matsayina na mutum, ina lura da irin gudunmawar da Adagunodo ya bai wa babbar jam’iyyarmu a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a Jihar Osun kuma ina murnar irin tasirin da ya yi a matsayinsa na Shugaban PDP na Kudu maso Yamma.
“Ina cikin bakin cikin rashinsa, ina tunawa da kyakkyawar mu’amala da muka yi tare.
“Addu’armu Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa ya kuma sa Adagunodo ya huta.