ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wani Babban Dalilin Da Ya Haifar Da Hargitsi A Kasar Sudan

by CMG Hausa
3 years ago
Sudan

Sanin kowa ne, kasar Amurka tana kallon kanta a matsayin “mai kare tsarin Demokuradiyya” a duniya. Sai dai yunkurin kasar na “kare Demokuradiyya” ya kan haddasa ta’asa a sauran kasashe.

Kwanan baya, na karanta wani bayanin da shafin yanar gizo na jaridar New York Times ta kasar Amurka ya watsa, mai taken “ Yadda yunkurin kasar Amurka na tabbatar da tsarin Demokuradiyya a Sudan ya haddasa yaki a kasar”.

  • Karuwar Cinikin Wajen Sin A Watanni 4 Na Farkon Bana Ta Kai Kaso 5.8 Bisa Dari Kan Na Makamancin Lokaci Na Bara

Marubucin wannan bayani ya ce, kasar Amurka ta dade tana kokarin mai da kasar Sudan wani misali na gwajin yada tsarin Demokuradiyya a sauran kasashe, inda ta yi ta shisshigi cikin harkokin siyasa na kasar. Sai dai kamar yadda ake cewa “Domin auki ake yin kunu ya komo ya rasa auki”, goyon bayan da kasar Amurka ta nuna wa manyan hafsoshin kasar Sudan ya sa su girman kai da kwadayin ikon mulki, lamarin da ya sa ake samun barkewar wutar yaki a kasar yanzu.

ADVERTISEMENT

Wannan bayani ya nuna yadda kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka yi tsokaci game da manufar kasar ta “yada tsarin Demokuradiyya” a duniya. Ra’ayin marubucin bayanin na “manufar kasar Amurka ta haddasa hargitsi a kasar Sudan” ya yi daidai, amma bai fayyace ainihin dalilin da ya sa ake samun wannan sakamako ba.

A ganinsa, idan kasar Amurka ta saka wa shugabannin sojojin kasar Sudan takunkumi a maimakon nuna musu goyon baya, to, za a iya tabbatar da tsarin Demokuradiyya a kasar. Sai dai, a hakika, yadda kasar Amurka take shisshigi a harkokin kasar Sudan, da fakewa da batun Demokuradiyya, shi ne babban dalilin da ya sa ake ta samun rikice-rikice a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

Tun da tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya kama mulki a shekarar 1989, kasar Amurka ta fara kokarin neman kawo karshen mulkinsa. Daga farkon shekarun 1990, kasar Amurka ta hure wa gamayyar kasa da kasa kunne, don su dakatar da samar da tallafi da rance ga kasar Sudan, bisa dalilin wai kasar na “keta hakkin dan Adam”.

Daga baya, kasar Amurka ta kara sanya wa kasar Sudan takunkumi, bisa zarginta da “nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda”. Matakan da kasar Amurka ta dauka sun sa Sudan zama wata kasa dake “rike da kwanon zinariya tana barace-barace”, ganin yadda kasar ta kasa raya tattalin arzikinta, inda ta kai har kashi 47% na al’ummar kasar sun tsunduma cikin tsananin talauci, duk da kasar na mallakar dimbin albarkatun kasa, ciki har da danyen mai.

Ban da matakan tattalin arziki, kasar Amurka ta kuma dauki matakai na siyasa, don neman hambarar da shugaba al-Bashir. Inda ta dade tana samar da tallafi ga dakaru masu adawa da gwamnatin Sudan, ciki har da dakarun yankin Darfur, da na yankin da aka fi samun danyen mai dake kudancin kasar. Lamarin da ya sa ake ta samun tashin hankali a kasar Sudan, da yukurin ballewar yankin kudancin kasar, wanda ya zama kasar Sudan ta Kudu daga bisani.

Wannan lamari ya sa kasar Sudan asarar kashi 70% na albarkatun mai, da fuskantar raguwar kudin shiga, da tsanantar yanayin koma bayan tattalin arziki, abun da ya sa dimbin jama’ar kasar aiwatar da zanga-zanga a wurare daban daban sakamakon matukar fushi. Daga baya, bisa goyon bayan da kasar Amurka ta bayar, Abdel Fattah al-Burhan, da sauran manyan hafsoshin rundunar sojan kasar suka kaddamar da juyin juya hali, wanda ya kai ga hambarar da shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Kasar Amurka ta kwashe shekaru 30 tana kokarin neman kawo karshen mulkin Omar al-Bashir, kuma a karshe ta samu biyan bukata. Sai dai hakan bai sa kasar Sudan karkata ga turbar Demokuradiyya ba.

Maimakon haka, an dade ana samun ja-in-ja tsakanin rukunonin sojan kasar. Har ma wannan yanayi ya sa an sa kafar wando daya, tare da juyewa zuwa wani babban tashin hankali mai tsanani yanzu. Sai dai sau da yawa mun ga abkuwar makamancin hakan, inda kasar Amurka ta yi shisshigi cikin harkokin gidan sauran kasashe, har ma ta hambarar da gwamnatocin kasashen, ta fakewa da “kare Demokuradiyya”, daga baya kuma kasashen suka fada cikin tarkon tashin hankali, da tabarbarewar tattalin arziki. Kuma da wuya su iya fitar da kansu daga cikin irin wannan tarko. Wannan lamari ya taba faruwa a kasashen Iraki, da Afghanistan, da kuma Libya.

Bayanin jaridar New York Times ya nuna cewa, ko Amurkawa ma ba su gamsu da matakan gwamnatin kasarsu na yada tsarin Demokuradiyya ba. A ganinsu, watakila za a iya daidaita aikin, ta hanyar kyautata dabarun shisshigi, misali nuna goyon baya, ko kuma sanya takunkumi kan sauran mutane.

Duk da haka, a matsayin mu na mutane na sauran kasashe, abin da muke son fada shi ne: Lokaci ya yi a kawo karshen girman kai na kasar Amurka. Idan kasar za ta iya girmama ikon mulkin kai na sauran kasashe, da daina yin shisshigi cikin harkokin gidansu, to, hakan zai iya zama gudunmowa mafi girma da kasar Amurka za a iya samar wa duniya, a fannin kare darajar Demokuradiyya. (Bello Wang)

Sudan
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
Daga Birnin Sin

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
Daga Birnin Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Next Post
FAAN Ta Bai Wa Kamfanonin Jirage Umarnin Kwashe Jiragensu Daga Filin Jirgin Saman Abuja

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.