Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da Sin, a matsayin muhimmin jigo na tabbatar da daidaito a duniya, kuma dangantakar sassan biyu na ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.
Shugaba Putin, ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a, yayin taron ’yan jarida na shekara-shekara da yake gudanarwa, inda ya ce Rasha da Sin sun ci gaba da aiwatar da jerin muhimman matakan hadin gwiwa a fannoni daban daban, inda darajar alakar cinikayyarsu ta kai tsakanin dalar Amurka biliyan 240 da 250.
Kazalika, Putin ya yi karin haske dangane da ci gaban da kasashen biyu suka samu, a fannin hadin gwiwar masana’antun manyan fasahohi, da ilimin kimiyya, da musayar al’adu da binciken sararin samaniya. Wannan ci gaba a cewarsa, ya shaida babban amincin dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce “Dukkanin wadannan dalilai ne, kamar yadda na sha jaddadawa, dake nuna yadda alakar Rasha da Sin ta zamo mai matukar muhimmanci ga samar da yanayin daidaito a duniya. Kuma Rasha a shirye take ta ci gaba da bunkasa alakarta da abokai na Sin a nan gaba”.
Yayin taron na ’yan jarida, Putin ya kuma bayyana aniyar Rasha ta ci gaba da yayata manufar shawo kan rikicin Ukraine ta hanyoyin lumana, yayin da ake aiwatar da matakan wanzar da tsaro da daidaito a shiyyarsu. Kazalika, shugaban na Rasha ya yi watsi da zargin cewa kasarsa barazana ce ga kasashen Turai, yana mai cewa irin wadannan zarge-zarge, ba su da tushe ko makama, kuma karairayi ne da wasu ke kitsawa.
Har ila yau, Putin ya yi maraba da ci gaban da aka samu dangane da tattaunawa da bangaren Amurka kan batun rikicin, yana mai fatan za a kai ga cimma irin wannan fahimtar juna tare da kasashen Turai. Kana ya ce Rasha a shirye take ta kawo karshen rikicinta da Ukraine, ta hanyar bin matakan lumana. (Saminu Alhassan)














