Kwanan baya, a yayin dake zantawa da dan jaridar babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, shugaban kasar Senegal Ousmane Sonko, ya nuna mamaki game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin zamanantar da kasa cikin shekaru 15 da suka gabata. Ya ce, tabbas kasar Sin ta cimma wannan nasara ne bisa babban karfinta na tsara aiki, da ladabtarwa da kuma babbar aniyarta.
Haka kuma, ya ce, kasar Sin ta hada aikin raya fasahar zamani da halin da kasar take ciki yadda ya kamata, tare da maimaita fannonin musamman da ci gaba na al’adun kasa. Kana, ya ce, yadda kasar Sin take yin kirkire-kirkire bisa halinta na musamman, ya kasance abun koyi ga kasa da kasa, musamman ma ga kasashen Afirka. (Mai Fassara: Maryam Yang)














