Da misalin da karfe 12 saura minti 1 na daren jiya wata girgizar kasa mai karfin maki 6.2 ta auku a gundumar Jishishan dake yankin Linxia a lardin Gansu a arewa maso yammacin kasar Sin, kana zurfinta ya kai kilomita 10. Ya zuwa yanzu, girgizar kasar ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 105 a Gansu, yayin da wasu fiye da 13 suka mutu a lardin Qinghai, tare da lalata hanyoyin samar da ruwa, da wutar lantarki, da sufuri, da sadarwa da sauran ababen more rayuwa.
Bayan abkuwar bala’in, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmanci tare da ba da umurnin cewa, dole ne a yi iyakacin kokarin ceton mutanen da mummunar girgizar kasar ta rutsa da su, da ba da jinya ga wadanda suka jikkata, da kokarin rage yawan wadanda suka ji rauni da rasa rayukansu.
Shi ma firaministan kasar Sin, Li Qiang ya bukaci a gaggauta tabbatar da yanayin bala’in, da gyara ababen more rayuwar da suka lalace cikin hanzari, da sake tsugunar da wadanda bala’in ya shafa yadda ya kamata, da gabatar da bayanai kan lokaci, a kuma kiyaye kwanciyar hankali a wuraren da bala’in ya shafa.
Yanzu haka, majalisar gudanarwar kasar Sin ta tura wata tawagar aiki zuwa wuraren da bala’in ya shafa don jagorantar ayyukan ceto da rage radadin bala’in, bisa urmunin shugabannin kasar. (Tasallah Yuan)