Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yabawa yankin musammam na Macao bisa nasarorin da ya samu cikin shekaru 5 da suka gabata.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a liyafar maraba da gwamnatin Macao ta shirya a jajibirin ranar cikar yankin shekaru 25 da dawowa karkashin ikon kasar Sin.
- Wike Ya Kwace Filin Buhari, Abbas, Akume Da Wasu Mutane 756 A Abuja
- Da Dumi-Dumi: An Yi Kutse A Shafin Hukumar Kididdiga Ta Kasa
A cewar Xi Jinping, wadannan nasarori na da alaka da yadda aka aiwatar da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” yadda ya kamata, da cikakken goyon baya daga gwamnatin tsakiyar kasar Sin da kuma yadda ake damawa da Macao din cikin harkokin duniya. Da kuma kokarin gwamnatin yankin na hada kan jama’ar dukkan bangarori.
Shugaban ya kuma bayyana wasu burika 3 da yake da su kan Macao, na farko, yankin Macao zai kara mayar da hankali kan manufofin ci gaban kasa kamar na gina yankin raya tattalin arziki na Guangdong-Hong Kong-Macao. Na biyu, bisa kauna da kishin Macao, za a kara bude kofa da tafiya da kowanne bangare da hada kai da jan hankalin masu basira daga fadin duniya, domin kara kyautata gina Macao. Na 3, ya kamata a zage damtse wajen aiwatar da gyare-gyare da kirkire-kirkire, da amfani da fa’idojin dake tattare da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” da samar da sabbin damarmakin raya yankin Macao.
Har ila yau da yammacin yau, shugaba Xi Jinping ya halarci liyafar murnar cikar Macao shekaru 25 da dawowa karkashin kasar Sin a babban dakin wasannin na Macao. (Fa’iza Mustapha)