A kwanakin baya, shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, ya zantawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, a birnin Mogadishu babban birnin kasar, inda ya bayyana cewa, karfafa bude kofa ga kasashen waje bisa babban matsayi da Sin ke yi, zai kara inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.
Ya ce a shekarar da muke ciki, ake cika shekaru 65 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Somaliya. A yayin da yake kimanta ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, shugaba Muhamud ya bayyana cewa, a cikin gomman shekarun da suka wuce, kasashen biyu sun kiyaye dangantakar abota, wadda ta ginu bisa mutunta juna, da amincewa da juna da gaske. A cewarsa, tun lokacin da Somaliya ta samu ’yancin kai, kasar Sin na ta nuna mata tsayayyen goyan baya. Ko da yake Somaliya ta sha wahalhalun tashe-tashen hankula a tsawon fiye da shekaru talatin, ciki har da yakin basasa da ma tabarbarewar lamura, amma dukkan manyan ayyukan hadin gwiwa tsakanin Somaliya da Sin, da kuma tallafin da kasar Sin ke ba ta, duk suna ci gaba da gudana. Kazalika, har kawo yanzu, da yawa daga irin wadannan sakamako na ci gaba da hidimtawa jama’ar kasar ta Somaliya, kamar asibitoci, da filayen wasanni, da kuma tagwayen hanyoyin mota da aka gina, duk wadannan har yanzu, suna bayar da hidima ga jama’ar kasar.
Haka zalika, shugaba Mohamud ya nuna cewa, yadda kasar Sin ke ci gaba da bude kofarta, da ma more fasahohin zamani tare da kasashen Afirka, ya samar da damammaki ga duniya, musamman ma ga nahiyar Afirka. Kana matakin Sin na bude kofa ga kasashen waje, ya samar da dama ga kasashen Afirka ta hada gwiwa da Sin a fannoni daban daban, tare kuma da ba su kwarin gwiwar inganta mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin. (Bilkisu Xin)














