Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya ce jarin kasar Sin na taimakawa wajen gaggauta ci gaban nahiyar Afirka, musamman ta fuskar samar da ababen more rayuwa da raya masana’antu.
Shugaba Museveni, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin bude taron hada-hadar kudaden samar da ci gaba na kasar Uganda na shekarar nan ta 2025, ya ce kamfanonin Sin masu zaman kansu da na gwamnati, sun taka rawar gani wajen samar da hanyoyin sufuri, da ayyukan bunkasa makamashi, ayyukan da ya bayyana a matsayin ginshikan bude kofofin raya nahiyar Afirka.
An dai kaddamar da taron na yini biyu ne a birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda, bisa taken “Sauya akalar Afirka ta hanyar bunkasa tsarin samar da kudade”. Taron ya kuma yi bitar irin rawar da masu zuba jari na kasar Sin suka taka wajen kafa yankunan masana’antu a sassan Afirka.
A cewar shugaba Museveni, irin wadannan yankunan masana’antu, baya ga tallafawa da suke yi wajen rage kashe kudaden shigo da hajoji, suna kuma samar da dubban guraben ayyukan yi ga matasan kasashen nahiyar.
Ya ce “Sabanin jagororin kasashen yamma, kasar Sin ta yi amfani da tarin damammakin da ta samu a Afirka, wajen zuba jari tare da alkawarta samar da gajiya mai dumbin yawa, don haka ya yi kira ga masu samar da lamuni na yammacin duniya da su dauki darasi daga kasar Sin, ta hanyar fadada samar da basussuka masu sauki ga kasashen Afirka, maimakon barin masu bayar da lamuni masu zaman kansu, suna sanya kudin ruwa mai tarin yawa kan lamunin da suke baiwa kasashen na Afirka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp