Shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema, ya zanta da wakilin kafar watsa labarai ta CGTN a kwanan baya, inda ya ce, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, wata shawara ce mai matukar muhimmanci.
A cewar shugaban, karkashin jagorancin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, kasar Zambia na kokarin hadin gwiwa tare da kasar Sin, a kokarin gina hanyoyin mota, da samar da kayayyakin more rayuwa, a bangaren samar da makamashi ba tare da gurbata muhalli ba. Haka zalika, ana tattauna yiwuwar yin garambawul kan tsohon layin dogo, wanda ya hada kasashen Tanzania da Zambia.
- Xi Jinping Ya Bukaci A Raya Masana’antu Masu Inganci
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Zhejiang
Shugaban ya ce yana fatan ganin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” za ta dore, saboda ba za ta haifar da kalubale ga duk wata kasa ba, sai dai alfanu. Ya ce, a baya a kan samu daukewar wutar lantarki a kasar Zambia, amma yanzu mutanen kasar sun saba da dorewar wutar lantarki. Hakan ya tabbata ne bisa hadin gwiwar da ake yi tsakanin Zambia da kasar ta Sin.
Zambia ta kulla wata yarjejeniya tare da kasar Sin, a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a shekarar 2018. (Bello Wang)