Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a ranar Litinin ya halarci bikin kaddamar da gina yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari, inda ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na bunkasa masana’antu a kudancin Afirka.
Kamfanin Xintai Resources na kasar Sin ne ya zuba jarin dala biliyan 3.6 a yankin masana’antu musamman na makamashi da karafa na kogin Palm da ke Beitbridge na lardin Matabeleland ta kudu, kuma za a aiwatar aikin a matakai biyar cikin shekaru 12, da nufin samar da kayayyakin da ake amfani da su na chromium da coke.
Mnangagwa ya ce, “Ina fatan aikin wannan yankin masana’antu na musamman, zai taka rawa a matsayin wani muhimmin tubali ga ci gaban masana’antu da zamanantar da al’ummarmu. Muna sa ran wannan aikin zai taimaka wajen ciyar da tattalin arzikin kasarmu gaba da kuma bude hanyoyin da ba a taba ganin irinsu ba wajen samar da ayyukan yi, da ci gaban fasaha, da ci gaban zamantakewa,”
Ya ce, aikin wani babban ci gaba ne ga hanyar da Zimbabwe ke bi wajen bunkasa masana’antu saboda ya hada aikin samar da makamashi da karafa, bangarori biyu masu muhimmanci da ke da damar sake fayyace yanayin masana’antu na kasar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp