Ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya gudanar da wani taro a jiya Juma’a, inda ya yi bitar daftarin ka’idojin da aka tsara da kuma matakan da suka dace da gina sabon yankin Xiongan na lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin cikin inganci. .
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS ne ya jagoranci taron.
Taron ya yi nuni da cewa, aikin da ya shafi Xiongan ya karkata zuwa ga gine-gine masu inganci da da manyan matakan gudanarwa. Don haka, yana da matukar muhimmanci a aiwatar da wani kunshin manufofin tallafawa da za su daidaita ci gaban aikin mayar da ayyukan da ba su da muhimmanci a Beijing babban birnin kasar zuwa sabon yanki. Taron ya kuma jaddada muhimmancin ayyukan gine-gine masu yawa a Xiongan. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp