Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bukaci jiga-jigan siyasar Arewa masu yunkurin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 da su kawar da burinsu su jira har zuwa 2031 lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Akume dai ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya halakar da tunaninsa na karbar mulki a shekarar 2027, inda ya ce idan Allah ya nufa zai zama shugaban, to zai iya lashe zabe ne kawai yana da shekaru 90 a duniya.
- Dattawan Arewa Sun Dukufa Wajen Warware Rikicin Siyasar Da Ta Kunno Kai A Kungiyar ACF
- Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Tare Da Ƙona Gidaje A Gombe
Akume, wanda ya yi magana a ranar Lahadin da ta gabata yayin wani shiri na TBC kan harkokin siyasa, ya ce har yanzu lokaci ne na Kudu wajen samar da shugaban kasa a 2027.
Sakataren gwamnatin tarayya wanda tsohon gwamnan Jihar Benuwai ne, ya ce Shugaba Tinubu bai rasa goyon bayan ‘yan Nijeriya ba, sakamakon kudirin gyara dokar haraji da sauran tsare-tsarensa na tattalin arziki da aka dauka a cikin watanni 17 na gwamnatinsa, ya kuma bayyana fatansa na cewa Tinubu zai jagoranci Nijeriya har na tsowon shekaru 8.
Ya kare kudirin sake fasalin haraji a matsayin wasu tsare-tsare masu kyau da za su taimaki kasar nan idan har majalisar dokoki ta amince da su.
Ya ce, “Ya kamata a bar Shugaba Tinubu a matsayinsa na dan Kudu ya sake yin wa’adi na biyu, ma’ana wadanda ke sa ido a kan smun shugabanci daga Arewa a 2027 su jira har 2031.
“Idan har Allah ya nufa Alhaji Atiku Abubakar zai zama shugaban Nijeriya, ko da yana da shekara 90, zai iya samun haka. Amma shi da sauran ’yan Arewa da ke sa ido kan ofishin shugaban kasa a 2027 su jira har Tinubu ya kammala wa’adinsa karo na biyu.”
Akume ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su kyale kudirin dokar sake fasalin haraji su daidaita ta hanyoyin da ake bukata na majalisa, yana mai cewa, “Suna da kyakkyawar manufa ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya.”