Shugabannin kasashen Afirka, da manyan jami’an kungiyoyin kasa da kasa, sun ci gaba da gabatar da sako zuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda suke nuna matukar alhini ga rasuwar Jiang Zemin.
A cikin sakon sa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce, marigayin ya jagoranci kasar Sin wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kama hanyar raya tattalin arziki yadda ya kamata, al’amarin da ya shaidawa duniya cewa, kasa za ta iya cimma burin raya tattalin arzikinta ta hanyar dogaro da kan ta. Buhari ya ce, nasarorin da marigayin ya samu a fannin tattalin arziki, suna da babban tasiri, wadanda ba za’a iya mantawa da su ba.
A nasa bangaren, shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto, ya ce a matsayinsa na wani gogaggen jami’in siyasa, Jiang Zemin ya dukufa ka’in da na’in, wajen aza tubalin tattalin arziki mai inganci, da tabbatar da zaman lafiya a duniya. Shugaban ya gabatar da jaje ga iyalai, da abokansa, gami da daukacin al’ummar kasar Sin baki daya.
Shi ma shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bayyana matukar alhini ga rasuwar tsohon shugaba Jiang, da girmama manyan nasarorin da ya samu, tare kuma da jajantawa al’ummar kasar ta Sin.
Sai kuma shugaban hukumar zartaswar tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, cewa ya yi shugaba Jiang Zemin, fitacce ne a fagen siyasar kasar Sin da ta dukkanin duniya, kuma rasuwar sa, babban rashi ne ga kasar Sin, da ma aminanta a duniya. Faki ya tausayawa gwamnati, da jama’ar kasar Sin, gami da iyalan marigayin, a madadin hukumar zartaswar AU.
Bugu da kari, jakadun wasu kasashen Afirka dake kasar Sin, ciki har da Najeriya, da Masar, da Aljeriya, da Mauritaniya, da Afirka ta Kudu, da Kamaru, da Senegal, su ma sun ziyarci ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, inda suka gabatar da matukar alhini ga rasuwar Jiang Zemin. (Murtala Zhang)