Duk da irin mawuyacin hali da babbar jam’iyyar adawa ta PDP take ciki, kan babban taronta na kasa a watan Nuwamba na wannan shekara, wani sabon rudani ya kara turnuke shugabannin jam’iyyar adawa sakamakon yadda jam’iyya mai mulki ta APC take zawarcin wasu gwamnonin PDP.
Rahotanni na nuna cewa jam’iyyar PDP na dab da rasa wani gwamna daga yankin kudu, wanda aka bayyana cewa a yanzu haka ya kammala shirye-shiryen sauya sheka shi da magoya bayansa.
- Kungiyar Masana’antu Ta Yi Fatali Da Sake Gabatar Da Haraji Na Kaso 4 Na Kwastom
- Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya
Jam’iyyar PDP na fama da matsaloli masu yawa wanda har ta kai ga rasa gwamnoni biyu wadanda suka koma jam’iyyar APC a cikin watannin da suka gabata, amma jam’iyya na ci gaba da kare kanbunta, yayin da aka tabbatar da cewa Shugaba kasa Bola Tinubu idan ya dawo daga daga ziyarar kasashen waje zai karbi wani gwamna na PDP wanda zai sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC.
“Zan iya tabbatar muku da cewa an kammala dukkan sharye-sherye na sauya shekan wani gwamna na PDP zuwa cikin APC. Ana ganin wannan gwamna a matsayin gwamna mai aiki tukuru da kwazo wanda yake da farin jini sosai a fagen siyasa a jiharsa. Abin da zan iya cewa a yanzu shi ne, ya kasance yana bangaren jihohin kuduncin Nijeriya ne. Mun gama dukan wasu shirye-shirye, muna jiran dawowar shugaban kasa daga kasashen waje don bayyana ficewarsa a hukumance,” in ji wata majiya.
Duk da cewa majiyar bai ambaci sunan gwamnan da abin ya shafa ba, idan zama a iya tunawa dai PDP tana da matukar karfi a bangaren siyasar kudancin Nijeriya. A kudu maso gabas, Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah ne kawai daga jam’iyyar PDP, yayin da a kudu maso kudu a yanzu haka dai akwai gwamnan da aka dakatar Sim Fubara na Jihar Ribas da Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri, yayin da kudu maso yamma ma tana da gwamnonin biyu ciki har da Seyi Makinde na Jihar Oyo da Ademola Adeleke na Jihar Osun.
APC za ta iya samun gagarumin rinjaye a jihohin kudu maso yamma idan Gwamna Mbah ya koma jam’iyyar, wanda shi ne kadai gwamnan PDP a wannan yanki, domin hakan zai daukaka yawan gwamnonin APC zuwa uku a wannan yanki. Haka nan lamarin zai iya faruwa a yankin kudu maso kudu idan Gwamna Fubara ko Gwamna Diri suka koma jam’iyyar APC daga jam’iyyar adawa ta PDP. Saboda haka, yawan gwamnonin a kudu maso kudu na iya karuwa daga biyar zuwa shida.
Majiyoyi da ke kusa da APC da PDP sun ce daya daga cikin gwamnonin PDP ya riga ya fice daga jam’iyyar PDP, kuma Shugaban kasa Tinubu zai karbi gwamnan zuwa APC lokacin da ya dawo daga tafiya.
Haka kuma majiya daga daya daga cikin gwamnonin yankin kudu ya tabbatar da cewa a daga cikin gwamnonin PDP na yankin kudu cewa ya riga ya fice daga PDP, kuma ko da yake gwamnan tun da farko yana son zama a cikin jam’iyyar don yin aiki tukuru wajen ganin an sake zaben Shugaban kasa Tinubu a 2027, an bayyana cewa ya dauki matakin barin PDP ya koma APC domin hakarsa ta cimma ruwa.
“Ya dai koma APC ne don samun nasarar ganin ya karfafa jam’iyyar a jihohin kudu da kuma samun karfi a arewa ta tsakiya da sauran yankunan Nijeriya gaban zaben 2027. Tuni dai mun karbi gwamnonin Delta da Akwa-Ibom a cikin jam’iyyar, kuma za mu ci gaba da amsar wasu a nan gaba,” in ji wata majiya.
An bayyana cewa sabon shirin da aka yi na ganin karin gwamnonin PDP sun fice zuwa jam’iyyar da ke mulki an kawo ta ne saboda abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar adawa ta ADC, inda aka fara samun labarai cewa jam’iyyar na iya amfani da tsarin karba-karba wajen fitar da dan takara a zaben 2027. An ruwaito cewa APC na shirin samun gagarumin nasara a kudu don rage tasirin da ake tunanin wani dan takara daga kudu zai iya yi, idan har dan takarar ADC ya fito daga wannan yankin.
Wata majiya ta ce, “Muna ganin cewa ADC na sake gabatar da wasu dubaru ta hanyoyi daban-daban. Idan wannan jam’iyyar ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga arewa maso gabas, hakan zai rage samun kuri’un kudancin kasar nan. Amma idan wannan jam’iyyar ta tsayar da wani dan takara daga kudu, hakan zai jawo hankalin shugaban da ke kan mulki, wanda zai bukaci ya tabbatar da karfin iko a wannan yanki. Wannan shi ne dalilin da ya sa jam’iyyar da kuma fadar shugaban kasar ba sa barin abubuwa su je ba tare da tsari ba ta hanyar mai da hankali kan zawarcin masu gwamnonin PDP masu tasiri.”
Kazalika, an bayyana cewa cikin gwamnonin da APC ke zawarci sun hada da Gwamnan Jihar Inugu, Peter Ndubuisi Mbah, Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang da Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp