Wata tawaga mai girma daga jam’iyyar PDP karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta na kasa, Ambasada Umar Damagum, ta kai ziyarar neman karin haske a hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Abuja ranar Talata.
Kamar yadda INEC ta wallafa a shafinta na facebook, tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da kwamishinoninta, manyan mataimaka, da kuma manyan daraktocin hukumar.
“Makasudin ziyarar a fili take: don tattaunawa da INEC kai tsaye kan matsalolin cikin gida da suka shafi jam’iyyar PDP, musamman ma wadanda ke bukatar tantance ka’idojin hukumar,” in ji INEC.
A jawabinsa na bude taron, Farfesa Yakubu ya jaddada aniyar INEC na gudanar da ayyukanta na doka, inda ya ce, “Aikinmu shi ne tabbatar da cewa an bi ka’ida.”