Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wa takwaransa na kasar Angola João Manuel Gonçalves Lourenço sakon taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu.
Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasashen biyu na nacewa ga sahihin zumunci tare da samun ci gaba cikin hadin kai, kazalika suna amincewa da goyon bayan juna kan muradunsu da manyan abubuwan dake jan hankalinsu.
A nasa bangare Lourenço ya ce, tun kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, ana ci gaba da samun bunkasuwar huldarsu, kana sun samu ci gaba mai armashi cikin hadin kai a bangarori daban-daban, sakamakon dake gamsar da bangarorin biyu.
Sannan an labarta cewa, kasar Sin za ta samar da rancen kudi domin taimakawa shirin samar da tsarin sadarwar intanet na kasar Angola, karkashin yarjejeniyar rance mai rangawame da aka rattabawa hannu jiya Laraba.
Karkashin yarjejeniyar, bankin kula da harkokin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin, zai samar da kudin da ya kai dala biliyan 249, domin shimfida hanyar sadarwar intanet mai tsawon kilomita 2,000 da za ta bi karkashin kasa da kuma wadda za ta hada kasar da yankin Cabinda da ruwa ya ratsa tsakaninsu, tare kuma da inganta baki dayan tsarin sadarwar kasar. (Amina Xu, Fa’iza Mustaph)