Yau Talata, shugaban kasar Sin da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun aikawa juna sakon murnar sabuwar shekara ta 2025.
A cikin sakonsa, Xi ya ce, Sin ba za ta canja sha’aninta na zurfafa yin kwaskwarima a gida da ingiza zamanintarwa iri na kasar Sin da ma gaggauta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya ba, duk da sauye-sauyen da ake fuskanta a duniya. Ya yi imanin cewa, kasashen biyu za su yi maraba da sabbin damammaki na hadin gwiwa a mabambantan bangarori.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2025
- Shugaba Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter
A cikin sakon nasa, Putin yana mai fatan kara hadin gwiwa da tuntubar Sin a dandaloli daban daban a duniya, ciki har da MDD da BRICS da SCO da G20 da sauransu.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Qiang da takwaransa na Rasha Mikhail Vladimirovich su ma sun mikawa juna sakon murnar sabuwar shekara. (Amina Xu)