Shugabar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento ta isa birnin Shanghai jiya Juma’a, inda ta bayyana fatanta na yin ziyarar da za ta kai har zuwa ranar 14 ga watan Yuni.
Ta bayyana cewa, al’ummar kasar Honduras na sa ran ziyarar ta zuwa kasar Sin, Castro ta ce amincewa da ka’idar Sin daya tak a duniya, da kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, da yin hadin gwiwa da kasar, na iya samar da damar samun ci gaba ga Honduras.
Ta ce, al’ummar Honduras sun yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen samun ci gaba, musamman ma kokarin da kasar ke yi wajen kawar da talauci, tana mai cewa kokarin kyautata rayuwar jama’ar kasar, ya dace da manufar kasashen biyu, ta kuma yi imanin cewa, dangantakar abokantaka da ke tsakanin Honduras da Sin, za ta yi tasiri wajen karfafa hadin kai da alakar al’ummomin kasashen biyu.
Ta kara da cewa, idan matasan kasar Honduras suka sami damar samun ilimi da koyon ilimin kimiyya da fasaha a kasar Sin, hakika za su iya ba da gudummawarsu wajen ginawa da raya kasar Honduras. (Mai fassarawa: Ibrahim)