Shugabar majalisar dokokin kasar Serbia Madam Ana Brnabic ta bayyana cewa, mutanen kasarta suna Allah-Allahr ganin ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai sake kai wa kasar ta Serbia, ta yadda kasar za ta samu damar karfafa zumunci tare da kasar Sin.
Madam Ana Brnabic ta bayyana haka ne lokacin da take hira da wakilin CMG a kwanan baya, dangane da ziyarar da shugaba Xi zai kai kasashen Faransa, da Serbia, da kuma Hungary, tsakanin ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Mayun da muke ciki. A cewar jami’ar ta kasar Serbia, shugaba Xi na kasar Sin na kallon Serbia a matsayin wata abokiyar hulda dake hadin gwiwa da kasar Sin cikin daidaituwa, ko da yake ba a iya kwatanta Serbia da kasar Sin a fannin girman kasa, da alkaluma ba. Hakan, a cewar Brnabic, ya nuna yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke kokarin cika alkawarinsa na tabbatar da zaman lafiya, da daidaituwa, gami da tsaro a duniya.(Bello Wang)