Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara.
“Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa Hassan a jawabinta ga kasar a karshen ziyararta a yankin Tanga. Tana mai cewa, babban kamfanin gine-gine mallakin kasar Sin wato China Harbor Engineering Compnay, shi ne ya yi aikin inganta tashar ta Tanga. Ta kara da cewa, inganta tashar da aka yi ya kuma samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da shirye-shiryen mayar da tashar ta zama cibiyar jigilar takin zamani da kayayyakin noma. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp