Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya kuma ce, kudin da Sin ta kashe a fannin tsaron kasa a bayyane yake, kuma yana da ma’ana da kuma dacewa.
Game da hadin gwiwar Sin da Rasha, Guo Jiakun ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu bai shafi wani bangare na uku ba, kuma wani karin bangare ba zai yi tasiri kan hadin gwiwar ba.
Bugu da kari, game da batun Amurka za ta kara tallafin aikin soja ga Indiya tun daga shekarar bana, Guo Jiakun ya ce, bai kamata a yi amfani da kasar Sin don bunkasa dangantaka da kuma gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ba, kuma kada a tayar da siyasar kungiya da kuma yaki tsakanin sassa daban daban.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp