Kungiyar masu sana’ar samar da manyan injuna ta kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, masana’antar ta samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024, biyo bayan shirin kasar na daukaka ingancin manyan injuna da ma dabarun raya masana’antar da aka dauka.
A shekarar 2024, ribar da manyan kamfanonin samar da manyan injuna suka samu ya karu kan na 2023 da kaso 6 cikin dari. Manyan kamfanonin na nufin wadanda suke samun kudin shigar da ya kai yuan miliyan 20 ko fiye, a shekara.
A bara, na’urorin samar da lantarki daga iska ne suka mamaye fiye da rabin kayayyakin samar da lantarki a kasar.
A shekarar 2024, cinikin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta ne ya dauki kaso 40.9 na jimilar cinikin motoci a kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp