Yau Litinin, mataimakin ministan ma’aikatar fadakar da jamaa ta kwamitin tsakiyar Jamiyyar Kwaminis ta Kasar Sin Sun Yeli, ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta shigo da salon neman ci gaba na sauran kasashe ba, kuma ba za ta amince wata kasa ta tilasta mata koyon salonta ba.
A yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin kara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, Sun Yeli ya yi bayani kan salon ci gaba iri na kasar Sin cikin sabon zamani. Ya ce, salon ci gaba na kasar Sin, shi ne irin ci gaba da kasar ta samu bisa yawan alummarta, da samar da wadata ga daukacin jamaa, da daidaita bunkasuwar tattalin arziki da aladu, da zaman jituwa a tsakanin muhallin hallitu da bil Adama, da kuma bin hanyar neman ci gaba cikin zaman lafiya.
Haka kuma, ya ce, kasar Sin tana son bayyana fasahohinta yadda ya kamata, ga kasashen dake son kara saninsu game da fasahohin kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)