• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a wani taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai da ya gudana yau Laraba, 4 ga watan Yuni cewa, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma batun yankin Taiwan sha’ani ne na harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ba ya kama da rikicin kasar Ukraine.

Don haka, kasar Sin tana adawa da duk wata magana ko wani take-take da ke kokarin kawo rudani ko yi wa batun Taiwan ungulu da kan zabo, kuma ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su mutunta manufar kasancewar Sin daya tilo a duniya ta hanyar bin ka’ idar a aikace da kuma mutunta ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar.

  • Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa 
  • An Samu Karuwar Kaso 2.7 Na Yawan Tafiye-Tafiye Zuwa Ketare Yayin Hutun Bikin Dragon Boat Na Kasar Sin

Kwanan baya, wasu shugabannin kasashen Turai sun kwatanta sha’anin Taiwan da batun Ukraine a yayin da suke halartar taron tattaunawa na Shangri-La, inda suka yi rika yin yamadidi da abin da suka kira da wai “barazanar kasar Sin” kan batun tekun kudancin kasar Sin, kuma suka yi nuni da cewa, kungiyar NATO tana da hujjar tsoma baki a yankin Asiya da tekun Fasifik.

Lin Jian ya yi wannan bayanin ne a cikin amsar da ya bayar kan tambayoyin da suka jibanci haka.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren tekun kudancin kasar Sin gaba daya yana cikin kwanciyar hankali kuma babu wata matsala game da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama da dukkan kasashe ke morewa bisa doka.

Ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin na dagewa kan amfani da tattaunawa da tuntubar juna wajen warware sabani da magance abubuwan da aka sha bamban a kai game da teku yadda ya kamata a tsakanin kasashen da abin ya shafa kai-tsaye, bisa mutunta hakikanin tarihi na gaskiya.

Haka nan, ya kamata kasashen da ba na yankin ba su mutunta kokarin da kasashen yankin suke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, maimakon haddasa fitina da haifar da zaman doya da manja. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.