A jiya Laraba ne Sin da Afirka suka sha alwashin kara inganta hadin gwiwar Sin da Afirka a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” (BRI), yayin da masu ruwa da tsaki suka yi alkawarin ba da tallafin kudi don kara inganta hadin gwiwar BRI.
Fathallah Sijilmassi, babban daraktan hukumar AU, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, babban taron karawa juna sani na tallafin kudi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka karkashin shawarar “Ziri daya da Hanya Daya”, ya zo a kan lokaci, kuma a daidai lokacin bikin cika shekaru goma na BRI.
A yayin da suke jawabi a wajen taron, wakilan bankin shigi da fici na Afirka, da bankin kasar Sin, da bankin inshorar kasar Sin, da kuma bankin Standard, sun yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka baki daya, musamman ma hadin gwiwar Sin da Afirka karkashin shawarar “Ziri daya da Hanya Daya”. (Mai fassara: Yahaya)