Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a jiya Juma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afirka wajen samar da sakamako masu inganci daga tsaren-tsaren ayyukan hadin gwiwa 10 da aka gabatar a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da aka gudanar a birnin Beijing a shekarar da ta gabata, tare da tabbatar da cewa, bangarorin biyu sun samu ci gaba kan hanyar zamanantarwa cikin sauri, da kwanciyar hankali.
Wang ya bayyana hakan ne a wata hirar da ya yi da kafafen yada labarai na kasar Sin bayan ziyarar da ya kai kasashen Namibia, Jamhuriyar Kongo, Chadi da Najeriya.
- Kasuwar ‘Yan Wasa: Omar Marmoush Na Dab Da Komawa Manchester City
- Za Mu Tabbatar Da Samun Kyakkyawar Alaka Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasuwar Kofar Ruwa – ‘Yanleman
Wang ya kara da cewa, shugaban Jamhuriyar Kongo Denis Sassou Nguesso da wasu shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, tsare-tsaren ayyukan hadin gwiwa guda 10, sun shafi dukkan fannoni na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da tinkarar kalubalen da Afirka ke fuskanta, da daidaita bukatun Afirka, kuma za su ba da goyon baya mai yawa ga ci gaba da farfadowar nahiyar ta Afirka.
Kazalika, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afirka wajen sa kaimi ga gudanar da harkokin daidaita sauyin yanayi a duniya, da kiyaye ka’idar “ana tare a zahiri amma an sha bamban a daukar alhaki”, kana ta bukaci kasashe masu ci gaba da su amince da nauyin da ke wuyansu na tarihi, da kuma sauke nauyin da aka rataya a wuyansu, da ba da tallafi na kudi, fasaha, da kara sanin makamar aiki ga kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.
A hadin gwiwa a fannin aikin gona kuwa, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana wasu muhimman fannoni guda biyar da kasar Sin za ta mai da hankali a kai, wadanda suka hada da samar da abinci, da rage fatara, da kara sanin makamar aiki, da saukaka harkokin kasuwanci, da sada zumunta, domin gaggauta aiwatar da sakamakon taron kolin FOCAC na Beijing a fannin aikin gona.
Da yake karin haske game da yadda kasashe masu tasowa ke samun ci gaba duk da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, Wang ya ce, Sin da Afirka su ne ginshikann ci gaba da farfado da kasashe masu tasowa na duniya, kuma suna da ra’ayin gina tsarin tafiyar da harkokin duniya mai adalci da daidaici.
Wang ya ci gada da cewa, a matsayinta na muhimmiyar aminiya kuma abokiyar huldar Afirka, kasar Sin za ta ci gaba da ba da goyon baya ga kasashen Afirka ba tare da kakkautawa ba, wajen gyara zaluncin da aka yi musu a tarihi, da yin kakkausar suka ga duk wani tsoma bakin waje a harkokin cikin gidan Afirka, tare da ba da shawarar samar da shirye-shirye na musamman don tinkarar matsalolin Afirka wajen yin kwaskwarima ga kwamitin sulhu na MDD. (Mohammed Yahaya)