Sin da Afrika sun bayyana aniyarsu ta kara hada hannu a bangaren horon fasahohi da sana’o’i wato TVET a takaice, domin tabbatar da nasarar shirin nahiyar Afrika na TVET na shekaru 10.
Wannan ya zo ne yayin taron karawa juna sani da kungiyar Tarayyar Afrika (AU) da tawagar kasar Sin a AU din suka shirya a ranar Laraba, a hedkwatar kungiyar da ke birnin Addis Ababa na Habasha.
A ranar Talata ne AU ta kaddamar da shirin TVET mai wa’adin shekaru 10, wanda wani tsari ne da aka sabunta domin karfafa gwiwar al’ummar Afrika, musammam matasan nahiyar da fasahohin da ake bukata na kirkire-kirkire da bunkasa ayyukan masana’antu da samar da ci gaba na bai daya.
Taron wanda ya hada jami’ai daga kungiyar AU da jami’an diplomasiyya daga kasashen Afrika da Sin da masana da sauran jami’ai a nahiyar, ya bayyana muhimmancin hada hadin gwiwar Sin da Afrika da shirin nahiyar na TVET. (Fa’iza Mustapha)