Yayin taron G20, gwamnatocin Sin da Afrika ta Kudu sun fitar da wata shawarar hadin gwiwa domin goyon bayan zamanantar da nahiyar Afrika, wadda ke da nufin mara wa kasashen Afrika baya wajen lalubo hanyar zamanantar da kansu da ta dace da yanayin kasashensu da cimma ci gaba mai dorewa.
Bangarorin biyu sun yi maraba da sabbin zabi da salon zamanantar da kasar Sin ya gabatar wa kasashe masu tasowa, ciki har da na Afrika. Sun kuma yaba da gagarumar gudunmuwa da dandalin FOCAC na tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika ya bayar ga burin zamanantar da kasashen Afrika cikin shekaru 25 da suka gabata bayan kafuwarsa da kuma jinjinawa manufar kasar Sin ta soke haraji da kaso 100 bisa 100 kan kayayyakin kasashen Afrika 53 da ke da huldar diplomasiyya da ita.
Gwamnatocin Sin da Afrika ta Kudu sun yi kira ga kasashen duniya su gaggauta yi wa tsare-tsaren kudi na duniya garambawul da bayar da taimakon kwararru ga kasashen Afrika da karfafa hadin gwiwa kan kayayyakin kare muhalli da makamashi mai tsafta da tabbatar da wadatar abinci da kiwon lafiya a Afrika da inganta raya kauyuka da daukaka ayyukan masana’antu da fadada musayar al’adu tsakanin jama’a da goyon bayan aikin zamanantar da kasashen Afrika.
An kammala taron na G20 ne jiya Lahadi a Johannesburg na Afrika ta Kudu. Cikin jawabinsa na rufe taron, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya bayyana godiya ga dukkan bangarori saboda goyon bayan da suka ba kasarsa a wa’adinta na shugabantar kungiyar. Ya kuma jaddada cewa, amincewar da aka yi da Sanarwar Shugabanni yayin taron, ya nuna jajircewar da ake da ita ta ci gaba da raya hulda tsakanin kasa da kasa. (FMM)














