Bayan zantawar baya bayan nan tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump ta wayar tarho, masharhanta da dama na ganin zurfafa musayar ra’ayoyi da suka yi dangane da alakar kasashen biyu, na iya taimakawa matuka wajen daga dangantakar sassan biyu zuwa sabon matsayi. Ana ganin tattaunawar na da fa’ida, kuma ta samar da tushe mai inganci na farfado da dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata.
Tarihi ya shaida yadda sassan kasa da kasa suka cimma nasarar daidaitawa, da sulhu bayan yake-yake da tashe-tashen hankula, kamar dai yadda kasashen duniya suka yi hadin gwiwa wajen kawo karshen mamaya, da danniya lokacin yakin duniya na biyu. Ruhin wannan hadaka da ta wakana shekaru 80 da suka gabata, ta ci gaba da wanzuwa kawo yanzu, musamman bisa tushen yarjejeniyoyin da suka kafa MDD, da rawar da take takawa a harkokin tabbatar da zaman lafiya, da dunkulewar kasashen duniya waje guda don cimma nasarar kyakkyawar rayuwa ga daukacin bil’adama.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Kakkaɓe Masu Amfani da Takardun Bogi a Ma’aikatunta
- Xi Ya Sanar Da Gudummawar Kasarsa Dangane Da Tunkarar Sauyin Yanayi Nan Zuwa 2035
Tabbas dunkulewa, da ci gaban kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, na da tasirin gaske ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewar bil’adama. Kuma a wannan lokaci da alakar kasashen duniya ke kara fuskantar yanayi mai sarkakiya, da rashin tabbas a yanayin tattalin arzikin duniya, da tashe-tashen hankula a shiyyoyi daban daban, kamata ya yi Sin da Amurka su yi amfani da wayewarsu ta tsawon tarihi, su fifita burikan bai daya na kasa da kasa, su kuma karfafa hadin gwiwa. Hakan ne kadai zai samu karbuwa tsakanin kasa da kasa.
Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba, kamar dai yadda muka gani a baya. Don haka, a wannan gaba da ake ta samun karin sakamakon kyautata muamala da gudanar da shawarwari, kamata ya yi bangaren Amurka ya kauracewa kakaba shingen cinikayya, wanda ka iya gurgunta nasarorin da aka riga aka cimma. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp