Ma’aikatar kula da harkokin kudi ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, kasashen Sin da Amurka sun amince manyan jami’ansu su ci gaba da musaya da tuntubar juna a fannin tattalin arziki, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin ganawarsu a tsibirin Bali.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne yayin da take tsokaci kan ziyarar kwanaki 4 da sakatariyar baitulmalin Amurka, Janet Yellen ta kawo kasar Sin.
Yayin tarukan da Yellen ta halarta kafin kammala ziyararta a jiya Lahadi, bangaren Sin ya bayyana fatan ganin Amurka ta nuna basira da sanin ya kamata wajen dawo da huldarsu bisa turbar da ta dace, ba tare da bata lokaci ba.
Ta kara da cewa, yanayin dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu na moriyar juna ce. Kuma Sin ta yi imanin cewa, raya dangantakar wata dama ce maimakon kalubale ga Amurka, haka kuma riba ce maimakon hadari. A cewar ma’aikatar, karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu shi ne abun da ake bukata kuma mafi dacewa a gare su baki daya. (Fa’iza)