Bayan tattaunawa ta kwanaki biyu, tawagogin Sin da Amurka, sun cimma matsaya dangane da tsare-tsaren warware batutuwan cinikayya da suke dora muhimmanci a kansu.
Bayan tattaunawar a jiya Asabar da yau Lahadi a birnin Kuala Lumpur, mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, wanda ya zanta da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayya na Amurka Jamieson Greer, ya ce makasudin alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, shi ne cimma moriyar juna da samun nasarar bai daya, kuma kasashen biyu na cin gajiya ne daga hadin gwiwa, yayin da suke tafka asara daga fito-na-fito.
Bisa jigon muhimmiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin tattaunawar da suka gudanar ta wayar tarho a farkon shekarar nan, tawagogin na Sin da Amurka, sun yi sahihiya, kuma zuzzurfar musayar ra’ayoyi kan muhimman batutuwan cinikayya da tattalin arziki da suke mayar da hankali a kansu, ciki har da matakan Amurka karkashin sashe na 301, masu nasaba da haraji kan jiragen ruwan Sin, da fannin tsare-tsaren ayyukan sufurin ruwa, da sashen kirar jiragen na ruwa, da tsawaita dage harajin ramuwar gayya, da haraji mai nasaba da sinadarin fentanyl, da hadin gwiwar tabbatar da dokoki, da cinikayyar amfanin gona, da sarrafa hada-hadar fitar da hajoji.
Kazalika, sassan biyu sun amince su yi aiki tare wajen tsara takamaiman matakai, da biyayya ga tsarin aiwatar da su a cikin gidan kowannensu.
Bugu da kari, karkashin jagorancin shugabanninsu, sassan biyu za su yi cikakken amfani da tsarin gudanar da shawarwari na Sin da Amurka, da wanzar da tattaunawa ta kut da kut, kan batutuwan da suke mayar da hankali a kansu a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya, da ingiza alakar tattalin arziki da cinikayya mai inganci, da daidaito, da dorewa, don gajiyar al’ummunsu, da samar da gudummawa ga ci gaban kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














