Wata sanarwa da ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta fitar, ta ce a jiya Jumma’a kasashen Sin da Amurka, sun sabunta yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya fannonin kimiyya da fasaha zuwa karin shekaru 5. A baya ma dai an sha sabunta wannan yarjejeniya da sassan biyu suka kwashe gomman shekaru suna aiwatarwa. Kuma sabon zangonta a wannan karo zai fara ne tun daga ranar 27 ga watan Agustan shekarar nan ta 2024.
Tun a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 1979, shugaban Sin na wancan lokaci Deng Xiaoping, da shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a karon farko, lokacin da Deng Xiaoping ke ziyara a kasar Amurka. Yarjejeniyar ta kasance irinta ta farko a matakin kasa da kasa da kasashen biyu suka rattabawa hannu, biyowa bayan kulla huldar dangantakar diflomasiyya tsakaninsu.
Nazari Kan Cututtuka 8 Da Ke Kama Zomo Da Hanyoyin Mangance Su
Tun daga lokacin ne kuma ake sabunta ta duk kusan shekaru biyar-biyar, inda take baiwa kasashen biyu damar yin musaya, a fannonin da suka shafi musayar kwarewar kimiyya da fasaha.
Kafin wannan karo, an tsawaita wa’adin yarjejeniyar da watanni 6 a watan Agustan bara, da kuma watan Fabrairun bana. (Saminu Alhassan)